audio
audioduration (s)
0.46
70.4
transcription
stringlengths
1
844
Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.
Gaisuwa ta ƙarshe
Tikikus shi ne ƙaunataccen ɗan’uwan nan, wanda ya yi aiki da aminci a hidimar Ubangiji tare da mu, zai kuwa faɗa muku dukan labari game da ni.
Ina aikansa shi a gare ku musamman domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.
Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunatacce da kuma amintaccen mai bin nan, wanda yake ɗaya daga cikinku.
Za su gaya muku dukan abin da yake faruwa a nan.
Aristarkus yana a kurkuku tare da ni.
Yana gaishe ku, haka ma Markus, wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas.
(Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu.)
Yesu, wannan da muke kira Yustus, shi ma yana gaisuwa.
Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah.
Sun kuma zama da taimako a gare ni.
Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa.
Kullum yana addu’a dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke.
Na tabbatar muku, cewa yana aiki ƙwarai dominku da kuma domin waɗanda suke a Lawodiseya da Hiyerafolis.
Luka ƙaunataccen likitan nan, da kuma Demas suna gaishe ku.
Ku miƙa gaisuwata ga ’yan’uwan da suke a Lawodiseya, musamman ga Nimfa da kuma ikkilisiyar da take taru a gidanta.
Bayan an karanta muku wannan wasiƙa, ku tabbata an karanta ta kuma a ikkilisiyar Lawodiseyawa; ku ma ku karanta wasiƙar da ta zo daga Lawodiseya.
Ku faɗa wa Arkiffus yă tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji.
Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna.
Ku tuna da sarƙoƙina.
Alherin Allah yă kasance tare da ku.
Ayyukan Manzanni 21
Zuwa Urushalima
Bayan muka rabu da su da ƙyar, sai muka shiga jirgin ruwa, muka miƙe zuwa Kos.
Kashegari muka tafi Rods daga can kuma muka je Fatara.
Sai muka sami wani jirgin ruwa da zai ƙetare zuwa Funisiya, sai muka shiga muka kama tafiya.
Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya.
Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa.
Da muka sami almajirai a can, sai muka zauna da su kwana bakwai.
Ta wurin Ruhu, suka yi ƙoƙari su hana Bulus wucewa zuwa Urushalima.
Amma da lokacin tashinmu ya yi, sai muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu.
Dukan almajirai da matansu da ’ya’yansu suka raka mu har bayan birni, a can kuwa a bakin teku muka durƙusa muka yi addu’a.
Bayan mun yi bankwana da juna, sai muka shiga jirgin ruwa, su kuwa suka koma gida.
Muka ci gaba da tafiyarmu daga Taya muka sauka a Tolemayis, inda muka gai da ’yan’uwa muka yi kwana ɗaya tare da su.
Da muka tashi kashegari, sai muka isa Kaisariya muka kuma sauka a gidan Filibus mai bishara, ɗaya daga cikin Bakwai ɗin nan.
Yana da ’ya’ya huɗu ’yan mata da ba su yi aure ba, waɗanda suka yi annabci.
Bayan muka yi ’yan kwanaki da dama a can, sai wani annabin da ake kira Agabus ya gangaro daga Yahudiya.
Da ya zo wurinmu, sai ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaura hannuwansa da ƙafafunsa da ita sa’an nan ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su daure mai wannan ɗamara su kuma ba da shi ga Al’ummai.’
Sa’ad da muka ji haka, sai mu da mutanen da suke can muka roƙi Bulus kada yă je Urushalima.
Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya?
A shirye nake ba ma a daure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”
Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yă yi nufinsa.”
Bayan haka, sai muka shirya muka kuma haura zuwa Urushalima.
Waɗansu almajirai daga Kaisariya suka raka mu suka kawo mu gidan Minason, inda za mu sauka.
Shi mutumin Saifurus ne kuma ɗaya daga cikin almajirai na farko.
Isowar Bulus a Urushalima
Sa’ad da muka zo Urushalima, ’yan’uwa suka karɓe mu da murna.
Kashegari Bulus da sauranmu muka tafi domin mu ga Yaƙub, dukan dattawan kuwa suna nan.
Bulus ya gaishe su ya kuma ba su rahoto dalla-dalla a kan abin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurin aikinsa.
Da suka ji haka, sai suka yabi Allah.
Sa’an nan suka ce wa Bulus, “Ka gani ɗan’uwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka.
An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Al’ummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ’ya’yansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga al’adunmu.
To, me za mu yi ke nan?
Lalle za su ji cewa ka iso, saboda haka, ka yi abin da muka faɗa maka.
Akwai mutum huɗu tare da mu da suka yi alkawari.
Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski.
Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar.
Game da Al’ummai masu bi kuwa, mun yi musu wasiƙa a kan shawararmu cewa su guji abincin da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka maƙure da kuma fasikanci.”
Kashegari, sai Bulus ya ɗauki mutanen ya kuma tsarkake kansa tare da su.
Sa’an nan ya tafi haikali domin yă sanar da ranar cikar tsarkakewarsu da kuma ranar da za a ba da sadaka domin kowannensu.
An kama Bulus
Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya suka ga Bulus a haikali.
Sai suka zuga taron duka, suka kama shi, suna ihu suna cewa “Mutanen Isra’ila ku taimake mu!
Ga mutumin da yake koya wa dukan mutane ko’ina cewa su ƙi mutanenmu da dokarmu da kuma wannan wuri.
Ban da haka ma, ya kawo Hellenawa a cikin filin haikali ya ƙazantar da wurin nan mai tsarki.”
(Dā ma can sun ga Turofimus mutumin Afisa a birni tare da Bulus suka yi tsammani Bulus ya kawo shi filin haikali.)
Duk birnin ya ruɗe, mutane suka zaburo da gudu daga kowane gefe.
Suka kama Bulus, suka ja shi daga haikali, nan da nan aka rurrufe ƙofofi.
Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse.
Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron.
Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.
Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a daure shi da sarƙoƙi biyu.
Sa’an nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi.
Waɗansu daga cikin taron suka ɗau kururuwa suna ce abu kaza, waɗansu kuma suna ce abu kaza, da yake shugaban ƙungiyar sojan ya kāsa samun ainihin tushen maganar saboda yawan hayaniyar, sai ya yi umarni a kai Bulus barikin soja.
Sa’ad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron.
Taron da suka bi suka dinga kururuwa, suna cewa, “A yi da shi!”
Bulus ya yi wa taron jawabi
Da sojoji suka kai gab da shigar da Bulus cikin bariki, sai ya ce wa shugaban ƙungiyar sojan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?”
Sai ya amsa ya ce, “Ka iya Girik ne?
Ba kai ba ne mutumin Masar nan da ya haddasa tawaye har ya yi jagorar ’yan ta’ada dubu huɗu zuwa hamada a shekarun baya?”
Bulus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne, daga Tarshish a Silisiya shahararren birnin nan.
In ka yarda bari in yi wa mutane magana.”
Da ya sami izini daga shugaban ƙungiyar sojan, sai Bulus ya tsaya a matakala, ya ɗaga wa taron hannu.
Da dukan suka yi shiru, sai ya ce musu da Arameyanci ,
Ayyukan Manzanni 3
Bitrus ya warkar da gurgu mai bara
Wata rana, Bitrus da Yohanna suna haurawa zuwa haikali a lokacin addu’a da ƙarfe uku na rana.
To, sai ga wani da aka haifa gurgu ana ɗauke da shi zuwa ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, inda akan ajiye kowace rana, don yă yi bara daga masu shigowa cikin filayen haikali.
Da ya ga Bitrus da Yohanna suna gab da shiga, sai ya roƙe su kuɗi.
Bitrus kuwa ya kafa masa ido, haka ma Yohanna.
Sai Bitrus ya ce, “Dube mu!”
Saboda haka mutumin ya mai da hankalinsa a kansu, yana fata samun wani abu daga gare su.
Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka.
A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.”
Ta wurin kama hannunsa na dama, ya taimake shi ya miƙe, nan take ƙafafu da idon sawun mutumin suka yi ƙarfi.
Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya.
Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah.
Sa’ad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah, sai suka gane cewa shi ne mutumin nan wanda dā yake zama yana bara a bakin ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, suka kuwa cika da mamaki da tsoro a kan abin da ya faru gare shi.