audio
audioduration (s) 0.46
70.4
| transcription
stringlengths 1
844
|
---|---|
1 Korintiyawa 5 |
|
A yi waje da ɗan’uwa mai halin lalata |
|
Ana ba da labari cewa ana lalata a cikinku, irin da ba a ma samu a cikin masu bautar gumaka. |
|
Har mutum yana kwana da matar mahaifinsa. |
|
Har ya zama muku abin taƙama! |
|
Ashe, bai kamata ku cika da baƙin ciki ku kuma daina zumunci da mutumin da yake aikata wannan ba? |
|
Ko da yake ba na nan tare da ku cikin jiki, ina tare da ku a cikin ruhu. |
|
Na riga na yanke wa wanda ya aikata wannan hukunci, kamar dai ina tare da ku. |
|
Saboda haka sa’ad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku. |
|
Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yă sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo. |
|
Ku daina taƙama. |
|
Ba ku san cewa ɗan ƙanƙanin yisti ne yakan sa dukan curin burodi yă kumbura ba? |
|
Ku kawar da tsohon yisti don ku zama kamar sabon curi da aka yi babu yisti yadda dai kuke. |
|
Gama an miƙa Kiristi Ɗan Ragon Bikin Ƙetarewarmu. |
|
Saboda haka, sai mu kiyaye Bikin ba da burodi mai tsohon yisti ba, ba kuma da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da burodi marar yisti na sahihanci da na gaskiya. |
|
Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata. |
|
Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya. |
|
Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. |
|
Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum. |
|
Me zai kai yin hukunci ga waɗanda ba ’yan ikkilisiya ba. |
|
Ai, waɗanda suke ’yan ikkilisiya ne za ku hukunta. |
|
Allah zai hukunta waɗanda ba namu ba. |
|
“Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.” |
|
2 Korintiyawa 7 |
|
Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah. |
|
Farin cikin Bulus |
|
Ku saki zuciya da mu. |
|
Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba. |
|
Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. |
|
Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. |
|
Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. |
|
Na ƙarfafa sosai. |
|
Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske. |
|
Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. |
|
Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus, ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. |
|
Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. |
|
Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai. |
|
Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. |
|
Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai. |
|
Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. |
|
Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba. |
|
Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa. |
|
Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. |
|
Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi. |
|
To, ko da yake na rubuta muku, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana. |
|
Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa. |
|
Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka. |
|
Na yi taƙama da ku a wurinsa, ba ku kuwa ba ni kunya ba. |
|
Kamar dai yadda dukan abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamarmu a kanku a gaban Titus ya zama gaskiya. |
|
Ƙaunar da yake yi muku ya ƙaru ƙwarai, duk sa’ad da yake tunawa da biyayyarku duka, da kuma irin yawan bangirman da kuka nuna masa lokacin da kuka karɓe shi. |
|
Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske. |
|
2 Korintiyawa 6 |
|
A matsayinmu na abokan aikin Allah, muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza. |
|
Gama ya ce, |
|
“A lokacin samun alherina, na ji ka, |
|
a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.” |
|
Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto. |
|
Wahalolin Bulus |
|
Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi. |
|
A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. |
|
Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. |
|
Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. |
|
Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya, da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. |
|
Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu, ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. |
|
Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya, mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba, cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. |
|
Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. |
|
Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne. |
|
Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai. |
|
Ba mu ƙi nuna muku ƙaunarmu ba, sai dai ku kuka ƙi nuna mana. |
|
A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu. |
|
Kada ku haɗa kai da marasa bi |
|
Kada ku haɗa kai da marasa bi. |
|
Gama me ya haɗa adalci da mugunta? |
|
Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? |
|
Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? |
|
Me ya haɗa mai bi da marar bi? |
|
Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? |
|
Gama mu haikalin Allah mai rai ne. |
|
Kamar yadda Allah ya ce, |
|
“Zan zauna tare da su, |
|
in yi tafiya a cikinsu, |
|
zan zama Allahnsu, |
|
su kuma za su zama mutanena.” |
|
Saboda haka, |
|
“Sai ku fito daga cikinsu, |
|
ku keɓe kanku, |
|
in ji Ubangiji. |
|
Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, |
|
zan kuma karɓe ku.” |
|
Kuma, |
|
“Zan zama Uba a gare ku, |
|
ku kuma za ku zama ’ya’yana, maza da mata, |
|
in ji Ubangiji Maɗaukaki.” |
|
Kolossiyawa 4 |
|
Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama. |
|
Ƙarin umarnai |
|
Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya. |
|
Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi. |
|
Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata. |
|
Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. |
End of preview. Expand
in Dataset Viewer.
README.md exists but content is empty.
- Downloads last month
- 2